Ban ce duk lalacewar Kirista ya fi ɗan takara Musulmi ba - Kashim Shettima


 

Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya nesanta kansa da wasu kalamai da ya ce "ba daidai ba ne, kuma masu hatsari" da wasu ke alaƙantawa da shi.


Wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran mataimakin shugaban ƙasar ya fitar, ta ruwaito Kashim Shettima na cewa kalaman da ake ambatawa ya furta lokacin wani taro da sanatoci ranar Lahadi wasu masu jamhuru ne suka kitsa a yunƙurinsu na nuna rashin dacewar 'yan takara Musulmai da ke neman shugabancin Majalisar dattijai.


Ya ce ba a bayyana kalaman a muhallin da aka yi su ba, kuma an canza musu ma'ana don kawai su dace da manufar masu zagon ƙasa ga burin al'ummar Najeriya na tabbatar da haɗin kan ƙasa.


Sanarwar ta ci gaba da cewa a yayin taron da 'yan majalisar dattijai masu gangamin ganin Sanata Godswill Akpabio da Sanata Barau Jibrin sun jagoranci majalisar dattijai ta goma, Kashim Shettima ya jaddada tsarin siyasar ƙasar inda ya yi nuni da cewa samun Kirista daga kudancin Najeriya da kuma wani Musulmi daga Arewaci shi ne zai tabbatar da daidaiton adalci don inganta muradin shigar da kowa a dama da shi a gwamnatin tarayya.


Ta ce kalaman Sanata Kashim Shettima sun taso ne sanadin wani gagarumin gangami game da rarrabuwar da ke tsakanin al'ummar ƙasar, kuma sun dace da alƙawarin jam'iyya mai mulki na ganin an dama da kowa a dukkan lardunan da rukunonin al'umma.


Ta ambato Sanata Shettima yana nunar da cewa, bisa la'akari da ganin shugaban Najeriya da mataimakinsa duk Musulmai ne, to ba zai kasance rashin kan gado ga 'yan majalisar ba, idan suka zaɓi ɗan takarar da ba Musulmi ba, ko da kuwa akwai Musulmin da ya fi cancanta, saboda tabbatar da daidaito.


A cewarsa, abin fargaba ne idan aka jirkita irin wannan roƙo maras harshen damo don nunar da cewa mataimakin shugaban ya ce duk lalacewar Kirista ya fi ɗan takara Musulmi.


Kashim Shettima ya ce rashin kan gado ne ma a ce mataimakin shugaban ƙasar wanda shi kansa Musulmi ne, zai iya ƙasƙantar da ƙwarewar ɗan'uwansa Musulmi a ƙasar da Musulmi ke jagoranta, har ma ya nuna nagartar shugabancin da babu kamarta, bisa doron da aka zaɓe su ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC a watan Fabrairun da ya wuce.

Post a Comment

Previous Post Next Post