Banbancin paid Ads da organic Ads

 


Yan kasuwa da yawa musamman masu kasuwanci a yanar gizo, suna yawan samun ruɗani wajen fahimtar tsarin tallar daya dace da kasuwancin su. 


Kafin mu tsunduma cikin bayani, zan so mu fara sanin tsarukan tallace-tallace da muke dasu. 


1- Organic Ads: wannan tsari ne da dan kasuwa ke tallar kayan shi da karfin shi na tuwo, ba tare daya biya ko sisi ba. 


2- Paid Ads: daga jin kalmar ma, kai kasan magana akeyi ta kuɗi, saboda tsari ne wanda dan kasuwa zai bada yan sulallan sa domin a tallata masa kasuwancin sa. 


Na san yanzu ku dan samu ilimi akan tsarin na tallace-tallace tallace. Yanzu kuma zamuyi alkafura mu nutsa acikin bayani. 


Tara abokan cinikayya ta hanyar organic ads, Abu ne mai matukar wahala. Saboda dan kasuwa sai yasha gwagwarmaya sosai wajen tattaro mutanen nan tare da tabbatar masu da cewa kaya shi nada inganci kwara dagaske, sannan fa zasu tari. 


Organic Ads, dai-dai yake da dan kasuwa mai zuwa rumfa ya kasa kayan shi, sannan kuma ya fara kada karaurawa domin a zo a saya. 


Organic ads Baya da wani tsari na shirya target audience, wannan yasa yin talla a wannan tsarin yake da matukar wahala. Saboda zaka iya yin talla ga mutanen da basu dace ba, kuma a lokacin da bai dace ba haka kuma a inda bai dace ba. 


Samun abokan cinikayya ta hanyar organic ads nada matukar wahala, amma sai dai kuma yina da wani alfanu mai matukar tasirin gaske. Wannan alfahun kuwa shine, duk wani abokin cinikayya daka samu, to dama ya zo ne dan wannan kasuwancin naka ,kuma yayi amanna tare da amincewa da ingancin kayan ka. A magana ta gaskiya, yina wahala a rasa abokin cinikayyar da aka samu ta hanyar yin organic ads, saboda dama shi, ya zo ne musamman domin kulla alamar kasuwanci da kai. 


A bangaren PAID ADS kuwa, wannan hanya ce dake da matukar sauki wajen tara audience. Saboda dan kasuwan yakan ware zunzurutun kudi ne domin a tallata masa kayan sa. Audience din suna iya taruwa da yawa har kuma a samu likes masu tarin yawa, to amma kuma fa ba dole bane su zama customers ba a wannan lokacin. 


Wasu audience din da aka tara ta hanyar paid Ads, ba suna taruwa bane dan wannan kasuwancin, a'a wasu flyer din da akayi tallarce ce ta burge su, wasu kuma video ko wakar dake background din tallar ce ta basu sha'awa, wasu kuma an dame su da tallar ne yasa suka yanke shawarar duba ko Meye aciki.


Wanda yayi paid Ads ya tara audience, akwai bukatar ya samu tsarin lead-on-ads funnel domin tabbatar da wadannan audience din daya tara sun zama abokan cinikayya. 


Paid Ads nada matukar tasiri sosai musamman a lokacin da dan kasuwa ke kokarin tallata sababin kayan da ya ƙera ko kuma wanda ya zuba a shago, haka kuma paid Ads na ta alfanu mai tarin yawa a lokacin da dan kasuwa keda wani target na na sayar da kaya a wani lokaci na musamman. 


Bugu da kari, idan har dan kasuwa ya bi tsarin lead-on-ads funnel, to zai kwashi garabasar ciniki mai tarin yawa daga audience din da paid Ads dinsa ya tara masa. Haka kuma zai tallata kayan sa ga wandanda suka dace a ko kuma lokacin daya dace kuma a inda ya dace. 


Organic ads da paid ads duka suna da amfani idan dan kasuwa yayi su a lokacin da suka dace. Samun ilimi akan harkar ko neman masu ilimi akan abun, shine kadai zai bama dan kasuwa damar kwasar romon damakwaradiyyar yin ciniki mai yawa a yanar gizo.

Post a Comment

Previous Post Next Post