HANYOYI 12
DA ZAKA BI DOMIN GUJEWA
AIKATA ZINA.
Babban Maganin da zai hanaka
yin Zina Insha Allahu, shine:
1. tsayuwa abisa tafarkin Allah da
gaskiya.
2. Cikakken Tsoron Allah a zuciya.
Tare da kwadayin samun
Rahamarsa.
3. Kulawa da yin Sallah akan
lokaci, kuma acikin Jam’I. Tare da
neman ilimin sanin Sallar.
4. Zikirin Allah safe da yamma
tare da neman tsarinsa daga
Sharrin Shaidan ako yaushe.
5. Tuna girman Allah da kuma
Kusancinsa gareka/gareki.
Yana tare dakai/dake alokacin da
kuke aikata wannan Kaba’irar
6.Tunowa da girman azabar da
Allah ya tanadar ma MAZINATA a
lahira.
7. Tunowa shaidan da kuma
kaidinsa da yake Qullawa domin
hallakar da ‘Yan Adam.
8. Gujewa kadaituwa da duk
wata Matar da ba Muharramarka
ba/ko Namijin da ba
Muharraminki ba.
9. Kaucewa kalle-kallen fina-finan
batsa. Ko kuma wakoki da
hotunan batsa.
10. Kaucewa abota ko Qawance
da duk wani saurayi Mazinaci ko
budurwa Mazinaciya.
11. Addu’ar neman tsari daga
munanan ayyuka, da mummunan
tunani.
“Allahumma inni a’uzu bika min
Munkaratil Akhlaaqi wal Af’aali
wal Ahwa’I.”
12. Ka tuna cewar Wannan da
zaka yi zinar da ita:
‘Yar wani ce.
Qanwar wani ce.
Diyar wani ce.
Watarana kuma zata zama Uwar
wani.
To yadda kayi Zina da ita, kaima
sai anyi Zina da Uwarka, ko
Qanwarka, ko Diyarka, ko ‘yar da
ka haifa.
Da fatan Allah shi kiyayemu daga
wannan mummunan aiki.
ZAUREN FIQHU.
Post a Comment