Komai Allah yayi daidai ne: Labarin wani sarki da hadiminsa

 Wani Sarki ne mai sha'awar farauta yake da hadiminsa mai tsananin tauhidi. A duk lokacin da wani abu ya samu Sarki na ɓacin rai, sai hadimin nan ya riƙa ba shi magana yana cewa, "komi Allah ya yi daidai ne."


Wata rana Sarki ya fita farauta da hadiminsa. Suna tafe cikin daji ba su da sanannen ciki, sai wata mahaukaciyar damisa ta far musu. Ta bangaje Sarki, ta haye ruwan cikinsa tana tumurmuza. Hadimin nan ya yi kukan kura, ya sa mashi ya tsire ta ya yarɓar gefe guda, ba ta ko shura ba ta kai takarda. Duk da haka sai da ta cizge wa Sarki yatsa.


Bayan sun komo gida, Sarki ya dubi hannunsa, ya ga yadda ya naƙasa haka, sai ransa ya ɓaci ya ce wa hadimin, "ashe wannan daidai ne ga Sarki ya zama ba shi da yatsa ɗaya?"


Hadimi ya ce, "ya Sarki, ka sani cewa komi Allah ya yi daidai ne."


Sarki ya fusata, ya sa aka jefa hadimi gidan jarun.


Bayan wasu 'yan kwanaki Sarki ya fita shi kaɗai zuwa ga farauta. Ya kutsa kai cikin daji ke nan sai ya yi taho-mu-gama da wasu matsafa, su kuma sun fito neman mutumin da za su yanka wa danko ya sha jini. 


Suka kama Sarki suka ƙunƙunce da asalwayin doki, suka jefa shi kuturi suka nufi gida. A kan hanya sai suka lura ashe ba shi da yatsa ɗaya, su kuwa ba su yanka wa gunki mutumin da ya naƙasa. Sai suka jefar da shi, suka juya neman wani.


Da Sarki ya dawo gida sai ya sa aka fito da hadimin nan da ke ɗaure. Ya ce masa, "ba ka sani ba fa yau na yi ɗaren shan yanka ba domin rashin yatsa ɗayan nan ba." Ya kwashe labari ya faɗa wa hadimi.


Hadimi ya ce, "da ma na gaya maka, Allah ya taimake ka, komi Allah ya yi daidai ne. Ka ga hatta ɗaure ni da ka sa aka yi, shi ma ya zama alheri gare ni"


Sarki ya ce, "ya aka yi ɗaure ka ya zama alheri?"


Hadimi ya ce, "da ba a ɗaure ni ba da tare matsafan nan za su kama mu. Idan sun sake ka, to ni kuwa za su yanka ni. Ka ga ɗaurin da ka yi mini ya kuɓutar da ni daga halaka. Don haka komi Allah ya yi daidai ne."


Sarki ya ce, "haƙiƙa Allah ba ya kuskure, komi ya yi daidai ne."


Post a Comment

Previous Post Next Post