Server computer che Amman da kwai banbanci stakanin shi Wanner computern (server) da normal computers da kuka sani(personal). Shi server ya fi computern da kuka sani stada, aiki da qarfi. Akan yi amfani dashi neh wajen aje tarin abubuwa kamar a che wajen ajiya. wannan servern kuma na wa client neh aiki ta hanyar shiga da fitar bayanai da wasu ayyukan, a yayin da aikin da servern ke yi kuma ake kiran shi da service, wato bada bayani da ayyuka.
Client su neh sauran computocin da Server kan taemaka wa. SERVER guda kan iya wa client da yawa aiki a yayin da kuma shi client kan iya amfani da servers daban daban wajen cin wa manufar sa.
_____
Muna da servers da dama da kuma aikin da suke yi
Bara mu dau ɓari daya mafi mahimmanci a fannin Server, wato Software Server, ga kuma abin da suke yi
1. Data Base Server
Data base server na amfani da data base applications neh ( applications din da ke ta'ammuli da bayani masu yawa, misali - asibiti.) Sukan amsa bayanai kuma su tura su inda ya dache domin bada amsa ko ajiya. Misalin applications dinnan sune MySQL, MongoDB da sauran su
↓
2. Mail Server
Su ke bada damar tura wasiqun E-mail (yanar giza) a tsakankanin clients /computers. Suna amfani neh da fasahar tura bayanai (protocols) irin su SMTP (Simple Mail Transfer Protocol) and POP3 (Post Office Protocol 3) ko kuma IMAP (Internet Message Access
Wannan kan qunshi dukkan bayanai (data) din da aka hada da wannan saqon kamar hotuna da sauran su.
↓
3.Web server
Web server ke bada daman raba bayanai a tsakankanin sahfukan yanar gizo. Servers din kan amshi saqonni daga yanar gizo sannan ya duba kuma ya tura abin da ya dache da abin da client ke so ko ke buqata, servers din na Amfani da fasahar raba bayanai (protocols) irin su HTTP (Hypertext Transfer Protocol) ko HTTPS (HTTP Secure). Misalin haka shine Apache HTTP Server da Nginx.
↓
4. Game server
Shi game server , wanda akan kira shi da Host. Shi ke da fasahar daukan masu wasa/game online tare da bayanan abubuwan da suke shigar wa , a yayin da servern ke amsa, ya haɗa ya kuma yi abinda ya dache da sauri kuma a kan lokachi
↓
5.Application server
Application server Kan amsa, su riqe su kuma yi amfani bayanan da kuka tura in kuka yi amfani da clients in ku/computer a yayin da kuka shigar da su. Su ke ingiza sadarwa stakanin Client da server, su ke aikin shige da fiche da kuma daukan lissafi masu wahala.
.
__________
A bangare daya kuma, Client server Kan yi aiki neh a kan starin request-response(nemi-ka-samu), wannan na nufin client kan tura abin da yake buqata sani ko abin da yake nema ei zuwa ga Server, a yayin da shi kuma servern zai amshi wannan saqon da client ya tura masa ya kuma yi aiki a kan sa, sannan kuma ya bada amsa ga abin da client din ya tura masa.
Akwai sauran abubuwa dayawa game da server irin su memory, drives, operating systems, networking, tsaro, aiki chikin sauqi da dai sauran su.
A nan zamu staya yau, da fatan kun qaru da wasu abubuwa ko ba yawa.
__________
✍️ Naim Hussain
# Husteemah
Post a Comment