Mun Dawo Da Tsarin Ci Gaba Da Bayar Da Tallafin Karatu Ga Dalibai Zuwa Waje – Abba
Sabon Gwamnar jihar Kano Eng. Abba Kabir Yusuf ya ce a cikin jawabin da ya gabatar ranar rantsuwa, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta dawo da tsarin nan na cigaba da bayar da tallafin karatu ga ɗaliban mu na jihar Kano domin samun manyan digiri a cikin gida da ƙasashen waje. A cikin watanni masu zuwa, za a fitar da ƙarin bayani, kuma za a fara aikin tantancewa domin fara wannan aiki.
Haka kuma, za a buɗe makarantun fasaha guda 44 da Makarantun koyon Ilimin Addinin Musulunci guda 44 da ke fadin kananan hukumominmu da Gwamnatin Sanata Kwankwaso ta kafa, wadanda gwamnatin da ta gabata ta rufe kuma ta yi watsi da su domin ci gaba da karatu da.
Source: hutudole
Post a Comment