Zafafan kalaman soyayya 2023 ASIYA

 ♥♥♥ASIYA♥♥♥


A---♥♥Amincin Allah ya kara tabbata ga mace ma'abociyar karamci hakuri da juriya barkanki da lokaci yake jarumata gwanar tsafta da kwalliya tabbas kece mace ta musamman a cikin rayuwata kece sarauniyata ina sonki


S---♥♥Sallma ce dauke da nau'in sakon zuciya wanda ya darsu a bakina nake jaddadashi agareki dare da rana kece masassafin dake iya sassarafa zuciya,kece wutar dake kone dukkan wata damuwata da ta addabi ruhina


 I---♥♥Ina kaunarki sonki yazamemin jini da tinaninki nake bacci dashi nake tashi abar yabona farincikina shine jin sautin muryarki domin itace abuna karshe danake ji kafin bacci idan nayi sa'a naganki a mafarkina haka ina tashi kece araina senaji muryarki nitsuwa ke dawowa gareni 


Y---♥♥Yanayinki na burgeni,so suturar rayuwane  kin lullubeni da sutura  mafi tsada aminci da tasirin da bazan taba iya rayuwa bake na ina alfahari da  samunki a rayuwata


A---♥♥Akwai wani dan adam yanada karfi kuma yanada rauni ni kece karfina haka kece rauni na ayayinda nake tare dake tabbas nidin me karfine amma dazarar nayi nesa dake nazama me rauni 


♥♥♥ ASIYA♥♥♥


Post a Comment

Previous Post Next Post