Kasuwar yan damfara (scammers) ta fara buɗewa a yan kwanakin nan saboda zuwan Network din 5G a Nigeria

 


Kasuwar yan damfara (scammers) ta fara buɗewa a yan kwanakin nan saboda zuwan Network din 5G a Nigeria.


Da yawan yan damfara (scammers) suna nan sun baza komar su domin damfarar duk wanda ya fada farkon su.


A hasashe mafi inganci, yan damfarar zasu kira ku ne ko kuma suyi maku sakon message akan cewa zasuyi maku upgrading na Network din ku daga 3G/4G zuwa 5G domin kara maku saurin Network a wayoyin Ku. Bugu da kari, suna iya cewa zasu baku kyautar data bayan sunyi maku upgrading din. 


Daga lokacin da kuka amince akan suyi maku upgrading, to zasu turo naku da One Time Password (OTP) ko kuma kuma lambobin Token a cikin layin ku, sannan kuma su bukaci cewa ku tura masu domin kammala aikin upgrading din. 


Wannan OPT din, yina iya yiwuwa daga bankin ka, social media handle ko kuma wani abu naka mai matukar amfani dake yanar gizo. Daga lokacin daga basu wadannan lambobin na OTP, to suna iya sace maka kudi a account na banki ya hanyar payment gateways, ko suyi maka hacking na social media handles ko kuma suyi maka kutse a wani abun naka mai amfani dake yanar gizo. Wanda hakan na iya jawo maka matsala da dama.


A yanzu haka an fara yin cyber kidnapping. Bana so nayi magana sosai a wannan wajen saboda tsaro da kulawa. Amma dai, kada ka yarda wani yace ka kashe wayar ka na tsawon lokaci saboda zai maka upgrading zuwa 5G. 


Kamfanonin layin da kuke amfani dashi ne kadai suke da hurumin yin maku upgrading. Dan haka mai bukatar ayi masa upgrading sai ya ziyarci ofishin kamfanin layin da yake amfani dashi ko kuma ya ziyarci jami'in su mafi kusa. 


Duk wayar da aka shiryata domin amsar network din 4G kadai, to babu yadda za'ayi ta koma 5G koda kuwa anyi upgrading din layin dake a cikin wayar zuwa 5G. Mai bukatar amfani da Network din 5G, sai ya siya wayar da aka kirkireta domin tayi amfani da 5G


 A kula sannan kuma a kiyaye da yan damfara.

Post a Comment

Previous Post Next Post