BAYANAI MASU MAHIMMANCI AKAN KODA ( KIDNEY)



AMFANIN KODA 

1. Cire abu marar amfani daga jini.
2. Daidaita ruwan jiki.
3. Daidaita lafiyar ala'ura ga maza da mata.
4. Daidaita yanayin jini da samar dashi.
5. Taimakawa wajen samuwar alli na kashi. 

MATSALAR KODA 

Matsalar koda kan faru idan ta sami matsala ko ta lalace gaba daya, sai abubuwa marasa amfani su rika taruwa a jiki. 

Lalacewar koda kan afku ba zato ba tsammani wanda in anyi magani matsalar kan kauce da wuri. 

Koda kan iya lalacewa ba'a sani ba har saita rube wanda hakan shine matakin karshe na ciwon don ba'a cika warkewa ba. 

BARAZANAR CIWON KODA. 

Afkuwar matsalar koda kan karu kamar sau 7 cikin dari a fadin duniya. A kasar mu najeriya, matsalar koda yakan kai kamar ga mutum dubu a cikin kowace miliyan daya, kuma a yanzu sun kai kamar mutane dubu dari da ashirin a wani bincike da aka gudanar. 

ABUBUWAN DA SUKAFI JAWO CIWON KODA. 

- Abubuwan dasukafi jawo ciwon sune kamar haka:
- Hawan jini,
- Kunburin koda,
- ciwon sugar 

Koda na iya lalacewa ta hanyoyi da dama har sukai matakin na karshe na ciwon koda har su sata rubewa. Akwai karin abubuwa dake sawa kamar yadda aka fada a baya sune: 

- Hawan jini.
- Kunburin koda.
- Ciwon suga.
- Marurun koda.
- Cutar jini na cikin kashi.
- Dakuma harbuwa da cuta. 

ALAMOMIN CIWON KODA 

-Yawan fitsari mai kala
- Fitsari mai kumfa
- Amai
- Ciwon kai
- Kaikai
- Kunburin kafafu ko ido.
- Haki
- Bushewar fatar jiki 

MATAKI DA MAGANI 

1. Fitar da fitsari ko ruwan daya lalace ta (Dialysis) da kuma guba ko datti da tsiyaye jini. 

2. Saka ruwa ta wajen cibiya (peritoneal dialysis). 

3. Canjen koda ta hanyar tiyata (fida) don akanyi dashen koda a kuma ajiye wacce aka cire akasan mara ta banagaren hagu. 

Koda da aka dasa takanyi aiki da gaggawa, amma wani lokaci akan dan sami jinkiri.
Allah yabamu Lafiya Ameen 

Allah cikin ikonsa muna bada magunguna daban daban ciki harda ciwon kodar kansa. Allah yasaka mudace ameen

Post a Comment

Previous Post Next Post