Cikakken bayani akan Mobile Bank Opay

 

Shin kasan asalin mai kamfanin OPAY da kuma CEO na kamfanin, da hanyoyin da ake Contacting nasu idan an samu matsala na Transactions? Kuma kasan gaskiyar jita-jitan da kakeji na zasu iya guduwa da kudin mutane ko makamancin haka?


Yahui Zhou shine mai kamfanin Mobile Banking na OPAY, kuma shine Chairman of the Board and Chief Executive Officer na kamfanin Opera, kuma fa mutumin nan Billionaire ne sosai kuma haziƙin ɗan kasuwa ne, yanada Degree a Mechanical Engineering da Masters a Optical Engineering a makarantar Tsinghua University a shekarar 1999 zuwa 2006. Dan kasar China ne.


Shi kuma Olu Akanmu shine CEO na bankin OPAY yanada Experience na shekaru sosai a bangaren Payments Industry kuma ya taɓa riƙe muƙamin Director of Business Development a kamfanoni da dama, Olu Akanmu Pharmacy ne yayi karatun Pharmacy ɗinsa a University of Ife (Obafemi Awolowo University). Da zaran kaje Branch na OPAY a Lagos zaka iya samun sa.

OPAY da wasu Mobile Banking da muke zuba kuɗaɗen mu a ciki bawai banki bane na wasu mutane da ba'a sani ba, idan yanzu haka OPAY suka gudu maka da kuɗinka cikin sauƙi za'a kamo su kuma su biyaka kuɗinka, sunada Licensed da CBN da yarjewar hukumar NDIC, babban bankin Nigeria ba kara zube yake ba bankuna Licensed ba sai banki ya cike Conditions ɗin da suka saka mashi kuma sai sun bada bilyoyin kudade kafin ma su samu Licensed din, haka zalika ba ta online bankunan zasu tattauna da CBN ba sai CBN tasan asalin mai bankin da sauran Information ɗin da suke buƙata, Abinda nakeso ku fahimta anan shine, Mobile Banking irinsu OPAY sauƙi ne a garemu fiyeda sauran bankunan, sune bankunan da zakayi Complain a Online suyi Responding ma Complain naka a cikin ƙananin lokaci, kuma sunada Features masu ƙyau a system nasu fiyeda na sauran bankuna.


Idan OPAY suka daina aiki yanzu haka, kai tsaye zaka iya kai ƙarar OPAY a CBN kuma za'a biyaka kuɗinka, dan haka You're Safe With OPAY, and Other Mobile Banking da sukeda Licensed da CBN.

Kar wani ya kawo maku kanzon kurege ku yarda, Duk wani labari da zaku samu kudinga tabbatar da sahihancinsa kuma kafin ku yada shi a duniya ku fara bincike tareda auna abun da mahangar ilimi.


OPAY sunada hanyoyin da ake tuntubarsu kamar haka:👇

Call: 0700 888 8328 or 01 8888328(wadannan Lambobin ana kiran OPAY dasu ne kawai idan an samu matsalar App nasu ko neman karin bayani akan Card nasu na cire kudi )


Call: 0700 888 8329 or 01 8888329(Wadannan Lambobin ana kiran OPAY dasu ne idan anason karin bayani ko kulla kasuwancin POS Business da machines nasu) kuma suna Available 24/7, zaka iya tuntubarsu a Whatsapp: - +2349165998936, ga kuma Email address nasu👇 customerservice@opay-inc.com


Sunada kafofin sadarwa na Social Media kamar haka:

1. Instagram:👇 https://www.instagram.com/opay.ng/

2. Twitter: 👇

https://twitter.com/OPay_NG

3. Facebook:👇 https://www.facebook.com/Nigeria.OPay https://www.facebook.com/opaymerchants

Offices nasu dake Nigeria, a lagos kawai sunada Offices guda 5.

1. Lagos: HQ: Alexander House, Otunba 

(a) Jobi Fele Way, Ikeja, Lagos, Nigeria.

(b). 103 Allen Avenue, Mosesola House, Ikeja.

(c). 78B Lagos Road Ikorodu.

(d). 4th Avenue A Close, Festac Town, Festac.

2. Abuja: No 34/36 Okotie Eboh Street Utako District.

3. Abeokuta,: Ogun Dolly House Opposite Laroy Hotel, Abiola Way.

4. Ibadan, Oyo Anjola Building Opposite Oando Filling Station, Iyana Cele Bus Stop, Along Sango Road, Mokola.

5. Osogbo, Osun: Opposite Technical Beside Arowolo Filling Station.

6. Jos, Plateau: Thilda’s Center, Shop 12 Opposite GIG Logistics Dadin Kowa 3rd Gate.

7. Kaduna: Asd City Mall Katsina Road By Independent Way.

8. Kano: Amana Plaza Second Floor beside Shoprite Zoo Road.


Allah yataimaka


Post a Comment

Previous Post Next Post