MAGANIN HAWAN JINI MAGANIN ULCER MAGANIN TSAKUWAR KODA

 


Don Annabin Rahma idan ka karanta ka turawa sauran yan uwa musulmi domi kowa ya amfana.


Wannan babban magani ne da yake magance cutuka kamar haka.


1. Ciwon Hanta

2. Ciwon koda/tsakowar koda.

3. Ulcer

4. Hawan jini

5. Majinar kirji

6. Ciwon kai


Dukkan wanda yake fama da daya daga cikin wadan nan cutuka ga magani sahihi guda daya da zai hada yayi amfani dashi,wanda insha Allah zai samu lafiya ya samu waraka a wajen Allah.


ABUBUWANDA ZAA NEMA


1. Ka samu rabin kofi na 'ya'yan Habbatus sauda.

2. Kaninfari cokali biyu, 

3. Yansun ma rabin kofi


Ahadasu adaka aturmi,sannan arika diban cokali biyu ana dafawa da ruwa kofi daya,Idan ya dahu sai abarshi ya huce, sannan azuba Zuma, arika sha.


Masu ciwon kai, Masu Olsa (Ulcer), Masu hawan Jini, Masu ciwon kirji, Masu tsakuwar koda, idan suna shan wannan zasu samu lafiya da izinin Allah. Za'a rika sha safe da yamma ne.


Allah yasa mu dace.


Share domin sauran yan uwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post