Matsalolin Da Ke Janyo Yawan Mutuwar Aure
Ba shakka yawan mace-macen aure ya ta'azzara a kasar Hausa ta yadda ya kasance babbar barazana ga iyayen Yarinya a duk lokacin da za su aurar da 'yarsu. Dalilin wannan magana shine, sau da yawa za ka ji iyaye na yiwa juna barka idan har su kai auren Yarinya kuma ba a ji matsala ba zuwa wani lokaci mai tsawo.
Kai, wannan matsala ba wai barazana ce, ga iyaye ba kadai, har da ma'auratan da kuma al'umma baki daya, saboda irin matsalar da take haifar wa ga zamantakewar al'umma.
A kokarin da Mujalla ke yi don fadakar da al'umma kan matsalolin da ke ci mu su tuwo a kwarya, a wannan makon, a fannin nan naku mai farin jini na "Daga yanar gizo" mun duba wannan batu, ga kuma wasu wallafe-wallafe da su ka gabata kan wannan matsala.
"Yawan mutuwar aure, matsala ce da ta zama ruwan dare a kasar Hausa. Alal misali, bincike na baya-baya da aka gudanar a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ya nuna cewa rabin auren da ake yi na karewa da saki". (BBC Hausa).
Mutane da yawa da aka tattauna da su dangane da wannan matsala sun kawo mabanbantan dalilai da ke haddasa yawan mutuwar aure a kasar Hausa. Yayin wasu ke danganta al'amarin da watsi da kyawawan al'adun Hausa, wasu kuwa na danganta yawan mutuwar auren da jahilci, Kwadayi, rashin tarbiyya, rashin sana'a daga bangaren maza, da laifin uwar miji ko muggan kawaye a wasu lokutan.
A wata makala da Mujallar "Premium Times Hausa" ta wallafa daga sheshin Malami na Jami'ar Bayaro ta Kano, Dr Usman Ibrahim Abubakar, me taken "Yawan mutuwar aure a kasar Hausa" wacce aka wallafa a ranar 6 ga watan Disambar shekara ta 2018, Malamin ya kasa abubuwan dake janyo mutuwar aure zuwa kashi biyu.
Malamin ya ce, Kashi na farko, abubuwa ne da ke faruwa tun kafin ayi aure, yayin da kashi na biyun ke faruwa lokacin da ma'auratan ke zaune a matsayin ango da amarya.
"Wadanda suke abkuwa kafin auren sun hada da rashin sanin ilmin aure, soyayyar karya da son abin duniya. A lokuta da dama soyayyar karya na gudana tsakanin namiji da mace, a inda daya daga cikinsu, baya son guda, amma sai yake/take nuna soyayyar karya. A irin wannan yana yin idan anyi auren, to ba zai dauki lokaci mai tsawo ba zai mutu, saboda tun farko an daura shine a bisa sigar karya". (Premium Times Hausa).
Hakanan malamin, ya kawo son abin Duniya daga cikin abin da ke kawo yawan mutuwar aure a kasar Hausa, inda ya ce, hakan na faruwa daga bangaren mazan da kuma matan. Ya kawo misalin yadda za ka ji saurayi na cewa, ba zai auri 'yar talaka ba, ya fi son 'yar me hanu da shuni da zai ke tallafa ma sa da abin duniya. To ka ga kenan bai shirya daukar nauyin yarinyar ba, maimakon haka shi ya na son ya yi aure ne don shi ma a dauki nauyinsa.
Daga bangaren 'yan-mata za ka ji su na cewa, su sai hadadden gaye za su aura, wasu 'yan-matan kuma su na kiransu "ready made" wai tuni yana aiki ko kasuwa, ya mallaki katafaren gida da mota da sauran kayan more rayuwa.
Don haka sai malamin ya ce, "A inda aka yi aure a bisa wannan tafarkin, to shima baya dadewa ma’auratan zasu fara samun matsala, saboda anyi auren ne kawai saboda son abin duniya. Ba wai soyayyar Allah da Annabi ba". (Premium Times Hausa).
Da ya koma kan abubuwan da ke kawo yawan mutuwar aure bayan an tare kuwa, sai ya ce, su na faruwa ne, ta bangarorin biyu, wato ta bangaren matar da kuma mijin.
Ya fara ne da bangaren matar, inda ya jero dalilan yawan mutuwar aure kamar haka: "kazanta, rashin iya girki, rashin gama abinci akan lokaci, da almubazanci.....rashin lafazi mai kyau/dadi ga mai gida, yawan fada da mutane ko dangin miji, yawan fita unguwa babu izni, yawan tambayar miji kudi, cin bashin mutane ba tare da izinin miji ba, da rashin ladabi ga miji, rage kudin cefane da zubin kudin adashi da su da sauransu". (Madogara ta sama).
Daga bangaren maza kuwa ya kawo abubuwan da ke kawo yawan mutuwar aure kamar haka: "rashin nuna kulawa da kwalliyar mata, da iya girkinta, tsafta, da sauran harkokinta na yau da kullum.......rashin saya mata kayan kwalliya da gyara jiki, yawan yi mata fada ba tare da binciken laifin da aka yi ba, yawan hantara da zagi.
Ya kara da cewa, "Akwai rashin fadar gaskiya a harkar zaman tare, da yawan kula mata, da rashin zaman gida tare da mu’amala da iyali. Abu na karshe da yafi ciwa mata tuwo a kwarya shine yawan amfani da waya a kodayaushe a cikin gida. Watau suna ganin cewa maza basu da lokacinn kula su a cikin gida, sai dai suyi ta danne-dannen wayar su".(Madogara ta sama).
Sai dai a wata tattaunawa da sashen Hausa na BBC ya yi da wasu mata don jin dalilin da ke kawo yawan mutuwar aure a kasar Hausa, matan sun zayyano abubuwan nan dake kasa a matsayin dalililan da ke haddasa yawan mutuwar auren.
"Kwadayin dukiya daga mahaifan yarinya da ita yarinyar kanta.
Karya daga bangaren maza
Rashin binciken asalin saurayi
Kazantar 'ya mace
Mugayen kawaye masu ba wa mace muguwar shawara
Rashin ladabi ga miji
Rashin hakuri daga bangaren maza"(BBC Hausa)
To, Me karatu ka ji daga bangaren maza, wato daga sheshin nmalamin Jami'a a matsayinsa na Uba kuma Malami, sai kuma daga bangaren iyaye mata. Idan ka duba dalilan da su ka bayar, za ka ga suna kama da juna.
Ita kuwa jaridar "Hausa Leadership" ta kalli al'amarin ne ta bangaren wasu al'adu da ke kawo yawan mutuwar aure a kasar Hausa. Jaridar ta wallafa wata makala me taken "Tasirin al'ada wajen kashe aure a kasar Hausa", kuma an wallafa wannan makala ne ranar 1 ga watan Satumbar shekara ta 2018.
Daga ciklin al'adun da aka rubuta dangane da yawan mutuwar aure a kasar Hausa a wannan makala akwai, al'adar tafiya renon ciki, ko kuma wankan gida a wasu guraren. Marubucin ya yi nuni da yadda al'adar ta banbanta daga gari zuwa wani.
A wasu guraren, dangin amarya ne ke zuwa su tafi da ita gidansu tun tana da ciki har zuwa ta haihu; shine ake kira renon ciki. Tun daga wannan lokacin da za su tafi da amarya gidansu ba za ta dawo gidan mijin ba, har sai ta haihu. Kuma ta na dawowa gidan mijin ne bayan ya biya wasu abubuwan al'ada idan ba haka ba kuwa aurensu na iya mutuwa.
"Idan amaryar ta samu ciki lokacin haihuwarta ya kusa ta kan tafi gidan mahaifanta ta haihu can, duk wata dawainiyar da ta shafi kula wa da ita da kuma abin da ta haifa a gidan mahaifanta a kan yi duk kuwa da yake gidansu mahaifan mijinta su ma ana tatsarsu kamar hanji sosai da sosai.
"Bayan ta haihu ne lokacin da ya kamata ace ita maijegon ya dace ta koma gidan mijinta, ba zata koma ba sai an yi mata wani abu wanda ake kira banti... maijegon ba za ta koma gidan mijin ba, sai har gidan shi angon sun sayi wasu kayayyaki, wani wurin ma idan abubuwan da ake bukata ba su cika ba ko da daya ne ya rage sai an kawo shi tukuna...
"Haka nan iyayenta za su shafa wa idonsu toka kiri da muzu su ki amince wa da ‘yar ta su ta koma gidan mijinta, idan kuma ba sa’a aka yi ba wannan al’amarin ana ji ana gani sai an raba shi ke nan, ana ji ana gani an bar maganar raya sunnar Annabi Muhammadu Salallahu alaihi wasallam". ( Hausa Leadership).
A wasu guraren kuwa, dangin amaryar na tafiya da ita ne bayan ta haihu kuma anyi suna a gidan mijin, sai a tafi da ita a matsayin za ta tafi wanka. To anan ma idan har ta tafi dawowarta sai yadda Allah ya yi.
Baya ga haka, sai mawallafin ya kawo wasu al'adu na zamani da ya ce, su na taimaka wa kwarai da gaske wajen yawan mutuwar aure a kasar Hausa. Al'adun zamani da ya kawo sun hada, da yadda ake matsawa mai son yin aure yin wasu al'adu da ke bukatar kudi, kuma ko shi ya na da kudin ko a'a. Ya kawo misali da yadda yanzu a kasar Hausa dole ne sai ango ya yi akwatuna ma su yawa, shi ma dai gwargwadon al'adar gari.
Yadda ake samun matsala a nan har ta kai ga mutuwar aure shine, a wasu lokutan akan tatuke miji tun kafin a kai ga yin aure, sai ka ga yayin da akai aure kuma ba shi da abin da zai dauki nauyin amryarsa, daga nan sai a fara samun korafi daga gare ta, ko kuma danginta, daga nan sai yawan rigingimu, wanda ke iya janyo mutuwar auren
Hakazalika, akwai wata al'ada da ake kira da 'Gara' wanda dangin Amarya ne ki yi su kaiwa gidan miji. Duk lokacin da aka samu rashin sa'a ba'a yiwa wannan amarya gara ba, to ta gamu da gori da kuma musgunawa daga dangin miji, yadda idan aka yi sake aure na mutuwa a dalilin hakan.
Ina Mafita ?
"Hanyoyin da za’abi ayi maganin yawan mutuwar aure a kasar Hausa sun hada da; gina aure a doron soyayyar gaskiya, rage son abin duniya, sanin ilimin auren kafin ayi shi. Sauran sun hada da iyaye su koyawa ‘ya’yansu mata tsafta, girki da ladabi da biyayya kafin aurar dasu.
"Mazaje su rinka ba wa matayensu kulawa ta musamman, da kuma yaba masu idan sunyi girki mai dadi ko kuma kwalliyar data burgesu. Sannan su kuma yi kokari suna zama tare da iyalensu a cikin gida. Har ila yau su daina amfani da wayarsu idan suna tare da iyalensu, sai dai idan kiransu akai a wayar to sai su amsa". (Premium Times Hausa).
"Ya kamata sarakuna da malamai su yi wani abu wanda zai taka rawa wajen binne duk wasu al’adun da ba su dace ba, saboda idan aka yi tunani suna haifar da raini maimakon kawo ci gaban al’umma.
Ba kuma wani lokacin da ya fi dacewa a daukin matakin da yafi dacewa kamar yanzu, a koma kan hanyoyin da suka dace, wadanda kuma me Alkur’ani ya ce, ko kuma Hadisin manzon Allah Sallallahu Alaihi wasallam ya ce, ba wai maganar wata al’adar da ba ta zama dole ba. ( Hausa Leadership).
Me karatu, a ganinka baya ga abubuwan da aka zayyana a sama, wadanne abubuwa ne ke haddasa yawan mutuwar aure a kasar Hausa ? Kuma ina mafita?.
Daga naku Sani Amadou Saban Kudi
Post a Comment