Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Sojin Nijar Ta Yanke Hulda Da Najeriya

 


Gwamnatin sojin Nijar ta ki tattaunawa da wakilan da kungiyar ECOWAS ta tura domin sulhu


Gwamnatin sojin Nijar ta kuma katse huldar diflomasiyya da babbar makwabciyarta Najeriya da Togo da kuma Amurka da tsohuwar uwargijiyar kasarsu Faransa — wadanda suke matsa musu su mayar da mulkin da ta kwace daga farar hula.


Gwamnatin sojin Nijar din ta kuma ki ganawa da wakilan da Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) ta tura domin tattaunawa da ita.


Wani daga cikin wakilan ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa kasa da awa 24 da isarsu birnin Yamai suka baro kasar Nijar, “ko kwana ba mu yi ba,” ballantana ganawa da Janar Abdourahamane Tiani kamar yadda aka tsara


A ranar Laraba ne ECOWAS ta tura wakilan nata, karkashin jagorancin tsohon shugaban mulki sojin Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar, domin tattaunawa da gwamnatin sojin da ta yi wa Shugaba Mohamed Bazoum juyin mulki.


Da farko dai gwamnatin Najeriya ta sanar cewa kwamitin na Abdulsalami Abubakar zai gana da Janar Tiani inda zai  gabatar wa gwamnatin sojin da ta yi juyin mulki a Nijar bukatun ECOWAS.


Kungiyar wadda Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu yake jagoranta, ta kakaba wa gwamnatin sojin ta Nijar takunkumin karya tattalin arziki, sannan a ranar Lahadi ta ba wa sojojin wa’adin mako guda su mika wa Bazoum mulkinsa.

Post a Comment

Previous Post Next Post