Bayani akan karatukan sheikh Jafar Mahmud Adam Kano

 




Domin yara masu tasowa, dake ganin videos din sheikh jafar na yawo a kafofin sadarwa. Bari nagayamuku wanene jafar:


- Yayi shekaru 31 yana koyarda Addinin Allah. 

- Ya kammala tafsirin Al-qurani har sau biyu a Maiduguri.

- Ya Karantar da littafin Kitabuttauhiid.

- Ya Karantar da littatafan Umdatul Ahkaam.

- Ya sauke littafin Arba'una Hadiith. 

- Ya sauke littafin tauhidi na Kashfusshubuhaat.

- Ya karantar da litaffin Bulugul Maraam,

- Ya Karantar da Riyaadussalihiin,

- Ya Karantar da Siiratun Nabawiy, 


- Ya Karantar da Ahkaamul Janaa'iz, -Ya Karantat da Siffatus Salaatun Nabiiy.

- Anyi kiyasi a duk najeria babu malamin da ake jin tafsirinsa kamar shi. 

- An masa kisan gilla a ranar juma'a

- An masa kisan gilla yana jan Sallar Asubahi. 

- Ya karantar da dubban al’umma a Kano, 

- Ya karantar da dubban al’umma a Maiduguri, 

- Ya karantar da dubban al’umma a Kaduna, 

- Ya karantar da dubban al’umma a Katsina da kuma,

- Ya karantar da dubban al’umma a Bauchi.


MANYA-MANYAN ALMAJIRAI DA MALLAM YA KOYAR KUMA SUNA YADA FATAWA IRIN TASA.


1.Malam Rabi'u Umar R/Lemo 

2.Malam Sani Abdullahi Alhamidi Dorayi 

3. Malam Abdullah Usman Gadon Kaya 

4. Malam Usman Sani Haruna 

5. Malam Ibrahim Abdullahi Sani.

6. Malam Ali Yunus Muhammad,

7. Dr. Salisu Shehu

8. Malam Shehu Hamisu Kura 9. Malam Anas Muhammad Madabo.


Neman ilimi da Mallam yayi lokacin yana raye.


- Marigayi Ja'afar ya fara karatunsa na allo a gidansu a Daura, a wurin mijin yayarsa, Malam Haruna, wanda kuma dan uwansu ne na jini.


- Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen wani Malam Umaru a wani gari “Koza” da ke Arewa da Daura a jihar Katsina. 


- Bayan sun zo Kano ne tare da wannan malami a 1971 sai ya zauna a makarantar Malam Abdullahi a cikin Fagge.


- Dama can Sheikh Ja'afar ya riga ya fara haddar Alkur'ani maigirma, wanda ya kammala a shekara ta 1978. 


- Bayan da Malamin ya haddace Alkur'ani ne sai ya ga bukatar ya samu ilmin Boko don haka ya fara karatun zamani a 1980.


- Malam Ja’afar ya shiga makarantar koyon Larabci ta mutanen kasar Misra a cibiyar yada al'adun kasar Misra (Egyptian Cultural Centre).


- Ya sake shiga makarantar Boko ta manya watau “Adult Evening Classes.”


- A 1983 ne Malamin ya kammala wadannan makarantu 2 na Boko da Arabiya, wanda daga nan ya samu shiga shiga makarantar GATC Gwale a 1984, har ya kammala a1988.


- Bayan shekara guda ne ya wuce Jami’ar Musulunci ta Madina.


A wannan babbar jami'ar musulunci ta Madinah ne Malamin ya karanta ilimin tafsiri da Ulumul Kur'an, wanda kuma ya kammala a shekara ta 1993. A wancan lokaci ne aka soma jin tafsirin sa na Al-Qur’ani a cikin Garin Maiduguri.


- Bayan nan Sheikh Ja’afar ya sami damar kammala karatunsa na digiri na biyu (Masters) a Jami’ar Musulunci ta Oundurman a kasar Sudan. 


- Kafin rasuwar Malamin, yayi nisa wajen karatunsa na PhD) a Jami’ar Usman Danfodio ta Sokoto.


Kafin rasuwarsa, Malam ya fara gagarumin aikin rubuce tafsirinsa a harshen Hausa a karkashin wannan cibiya (Sheikh Ja'afar Islamic Documentation Centre).


Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam ya rasu ranar juma'a 26/Rabii'u Awwal/1428 (daidai da 13/04/2007). Malamin ya rasu ya bar mata biyu, da 'yaya shida, yayin da aka haifa masa ta bakwai kwanaki 58 daidai bayan an yi masa kisan gilla.


Fatawowin Sheik Jaafar sunci gaba da yaduwa fiye da lokacin da yake raye.


Allah ya ji kan sa ya gafarta masa, ya saka masa da gidan Aljannatul-firdaus.


Alhassan Mai Lafia

Post a Comment

Previous Post Next Post