Matasa da dama (maza da mata) suna yawan tambaya ta shawara akan wace sana'a ya dace su yi a wannan lokaci.
To ga shawara ba sana'a kadai ba, har da kasuwanci da kuma irin course din da ya dace ka karanta a makaranta a wannan zamani.
SANA'A
1. Wanki da Guga na Zamani: Irin wanda aka zamanantar, har booking ake online, ana amfani da engine na wanki a yi guga mai kyau a saka a leda. Idan ka kai Boss sai dai ka dauki yara ka koma gefe kana bada Umurni.
2. Mayar da kayan gona gari: Zamani ya zo fasahar mayar da ababen gona da dama gari, ta hanyar busarwa da nikawa, kamar dankali, rogo, masara, gero da makamantansu, a garuruwan dake da manayan shaguna, yanzu packaging nasu ake ana sayarwa.
3. UBER DRIVER: Taxi ta zamani, da motarka lafiyayya mai kyau a yanzu sai kayi aiki a manyan garuruwa irinsu Kano, Kaduna, Abuja ba mai gane sana'a ka ke, kana cikin AC kuma kana kama kaya.
4. Kiwon kwaɗi: Kwarai kuwa kiwon kwaɗi, a yankinmu ba a damu da wannan sana'a ba, kasancewa babu masu cin kwaɗi sosai a nan. Amma ina tabbatar maka idan ka samu wadataccen wuri ka fara wannan sana'a, kana jigila kana kaiwa inda suka bukata zaka sha mamaki.
5. Ga ƴan uwa mata, Shagon gyaran ƙafa da yankan farce na zamani: wannan sana'a ce da matan masu shi, ke nema ayi masu, musamman idan aka ƙayata wurin, ana samu arziki ƙwarai a ciki.
6. Delivery: Musamman garuruwa irin namu sun yi ƙaranci. Kana da ɗan babur ɗinka, sai ka nemi 'yan kasuwa ƙanana da manya, idan suna bukatar aika sako a unguwanni su nemaka, kamin ɗan lokaci mutane da dama sun sanka akan wannan aiki.
7. Affiliation: Idan kai ɗan boko ne, ka iya zuwa manyan garuruwan kasuwanci kamar su Kano da Lagos, ka nemi zama dillalin wani kamfani. Idan ka dawo gida ka nemi 'yan kasuwa ko ɗaiɗaikun mutane da ke da bukatar waɗannan ababe ka tallata masu, kamfani ya cire maka riba idan ka samo masa customers. Matukar aka samu aminci da gaskiya wannan babbar harka ce.
8. Idan kana zaune kusa da inda al'umma da dama ke taruwa, kamar Stadium, ko wani babban super market, ko Asibiti ko Kasuwa, ka buɗe wurin wankin mota na zamani da ake amfani da engine da sauran sanadarai da ke sa mota haske da kyalli. Akwai samu a ciki.
9. Cleaning: Shara da wanke wanke. Shi ma wannan an zamanantar da shi. Idan kana zaune a manyan garuruwa, zaka buɗe kamfani ka ɗauki yara maza da mata da suka kware a shara da tsaftacce wurare, ka yi masu uniform, ka nemi offices, ma'aikatu da kamfuna, abaka kwangilar shaftace wurin a kowace safiya. Zaka tura yaranka suna kula da duk inda ka samu aiki. A fita tunda asuba a tsaftace wurin ta hanyar shara da gogewa da tsaftace banɗakai da sauransu. Akwai samu a wannan harka.
10. Security guard, idan Allah ya sa kana da masaniya a harkan tsaro, sai ka buɗe kamfani, ka samu matasa ka basu horo, a samu uniform masu kyau. Sai ka nemi aiki a ma'aikatu da kamfuna inda zaka dinga tura masu yara da zasu kula da tsare kofofi na shiga da fice. Idan ka ƙulla yarjejeniya mai kyau. Akwai samu a ciki.
Duk kasuwanci da ka ke bukatar farawa, ka nemi waɗanda suka jima a ciki, ka yi bincike mai zurfi, ka kuma yi hakuri. Ba a fara kasuwanci lokaci ɗaya a samu manyan kuɗi, sai an yi hakuri zuwa wani lokaci da za a sanka kuma a fahimci abin da ka ke iyawa.
'YAN MAKARANTA
Saurara ka ji ya kai matashi, a wannan zamani ba magana ake a tafi jami'a ko college of education a karanci courses masu sauƙi bane. Magana ce ta duba abin da zamani ke bukata kamar ilimin computer, Finances, Engineering, Medicine, Accounting da sauran manyan course da duniya ke bukata. Idan ka biyewa sauki a wannan zamani babu inda zaka tsinci kanka sai a ruwa kusa da kada😯
Kuma kada ka kuskura, kace sai ka gama makaranta zaka fara neman aiki. Nemi koda volunteer ne a wata ma'aikata ko kamfani kana zuwa a lokacin hutu. Ko ka koyi wata sana'ar hannu. Ko da zaka gama karatu, aƙalla kana da wani abu a hannu kamin wani babban abu ya faɗo.
Post a Comment